BIsa Dukkan Alamu: Ganduje Ya Raina Majalisar Dokokin Jahar Kano

GANDUJE YA RAINA MAJALISAR DOKOKIN JAHAR KANO.
Kwamitin Binciken Da Majalisar Dokokin Jahar Kano Ta Kafa Karkashin Jagorancin Dan Majalisar Jaha Mai Wakiltar Karamar Hukumar Birni, Hon. Bappah Babba Dan Agundi, Akan Yayi Mata Binciken Wani Fefen Bidiyo Da Akaga Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje Yana Karbar Wasu Daloli Da Ake Zargin Rashawa Yake Karba Daga Hannun Yan Kwangila. Wanda Wani Dan Jarida Mai Suna Jaafar Jaafar Ya Fara Wallafa Bidiyon.
Majalisar Ta Fara Aikinta, Kuma Ranar Alhamis 25/10/2018 Dan Jarida Jaafar Yazo Gaban Majalisar Domin Amsa Gayyatar Da Majalisar Tayi Masa, Anyi Masa Tambayoyi Kuma Ya Bada Amsa, Daga Karshe Ya Basu Copy Din Fefen Bidiyon Domin Suje Su Sake Binciken Bidiyon.
Yau Juma’a 02/11/2018 Ake Saran Ganduje Zai Bayyana A Gaban Majalisar, Domin Shima Sun Aika Masa Da Takardar Gayyata Kuma Harma Ya Amsa Zaizo Kamar Yadda Suka Bukata.
Amma Kawai Sai Akaga Kwamishinan Yada Labarai Da Kuma Attorney General Na Jahar Kano Sun Bayyana A Majalisar Da Sunan Zasu Wakilci Gwamnan, Saboda Acikin Jerin Abubuwan Dazai Gudanar Yau Babu Zuwa Majalisa.
Abin Tambaya Anan Shine: Me Yasa Ganduje Ya Amsa Gayyatar Bayan Yasan Yau Bashi Da Damar Zuwa Majalisa ?
Yanzu Dai Al’ummar Jahar Kano Alkalanci Ya Rage Namu, Domin Anyi Yunwa Halin Kowa Ya Fito, Sai Musan Irin Mutanen Da Zamu Dinga Zaba Su Shugabancemu. Ubangiji Allah Ka Bamu Shugabanni Nagari.No comments:

Post a Comment