Boren `Yan Shi`a: Babban Sufeton ‘Yan Sanda Ya Bukaci `Yan Sanda Da Daura Damara

Boren ‘Yan Shi’a: Babban Sufeton ‘Yan Sanda Ya Bukaci ‘Yan Sanda Da Daura Damara

Rahotanni sun bayyana cewa babban sufeto janar na ‘yan sandan Nijeriya Ibrahim Idris ya umurci dukkanin kwamishinonin ýan sanda da su kasance cikin shiri kan ayyukan mambobin kungiyar yan Shi’a.

Sufeto Janar din ya bayyana haka a wata sanarwa da kakakin mukadashin DCP Jimoh Moshood ya bayyana a Abuja a jiya Talata, 30 ga watan Oktoba wanda ke cewa an umurci kwashinonin musamman masu fuskantar barazana daga ýan Shi’a da su dauki mataki a kan su sosai kamar yadda doka ta tanadar.

“An bukaci su dauki matakin da ya dace a kansu daidai da doka sannan su hana yan kungiyar karya doka a jihohin,” inji shi.

Moshood ya ce, sufeto janar na yan sandan ya bada umarnin da a yi bincike sosai sannan a hukunta mambobin kungiyar 400 da aka kama a Abuja a ranar Talata kan zargin haddasa husuma.

Ya kuma bayyana cewa za’a gurfanar da su a kotu a matsayin yan ta’adda.

Sufeto janar din ya yi tir da harin da kungiyar suka kai ma yan sanda tare da kona motar yan sandan, inda yayi gargadin cewa rundunar ba za ta lamunci karya doka da matsi daga kowani kungiya ba.

No comments:

Post a Comment