Dalla-Dalla: Yadda DSS Suka Gano Oshiomhole Yana Amsar Kudaden Mutane

Dalla-Dalla: Yadda DSS suka gano Oshiomhole yana amsar kudaden mutane

Kamar yadda majiyar mu ta ruwaito, hukumar DSS ta yi rubutu ga shugaban kasa akan badakalar da shugaban jam’iyyar APC ta kasa yake yi. Hukumar ta bukaci shugaban kasan da ya dau matakin da ya dace.

Ana zargin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, da karbar dala miliyan 55 na cin hanci akan zaben fidda gwani na jam’iyyar da akayi a fadin kasar.

Bayan da hukumar ta mika rahoton ga shugaban kasa, ta kuma mika ga hukumar yaki da rashawa EFCC.

“Jimillar dala miliyan 55 ne ake zargin Adams Oshiomhole da karba. Wasu yan jam’iyyar ma sunce dala miliyan 80 ne” inji wata majiyar.

Kamar yadda rahoton ya nuna, dala miliyan 17 ya karba daga jihar Zamfara :

Dala miliyan 10 nashi, dala miliyan 7 kuma na Farouk Adamu,tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Niyi Adebayo, tsohon gwamnan jihar Ekiti da sauran manyan jam’iyyar. “Adamu ne ya wakilta don karbar kudin, ” inji majiyar mu.

“Hope Uzodinma, mai takarar gwamna a jihar Imo karkashin jam’iyyar APC, ya bada dala miliyan 3, Rochas Okorocha, gwamnan jihar ya bada dala 500,000 amma ba’a karba ba. Dapo Abiodun, Dan takarar gwamnan jihar Ogun ya biya dala miliyan 5.

Hukumar DSS tace wasu daga cikin kudaden an tura ne ta asusun bankin ‘yar yayar Oshiomhole.

No comments:

Post a Comment