Dan Jarida A Jihar Kaduna Ya Rasa Aikinsa Saboda Ya Yabi Shugaba Buhari

Dan Jarida A Jihar Kaduna Ya Rasa Aikinsa Saboda Ya Yabi Shugaba Buhari
Tashar yada labarai a Kaduna, DITV-Alheri Radio, mallakin tsohon na hannun daman Shugaba Muhammadu Buhari, Hakim Baba-Ahmed, ta kori ma’aikacinta Umar Ridwan saboda ya yabi Gwamnatin Buhari a shafinsa na facebook.
Majiyarmu ta Daily Nigerian ta ruwaito Mista Baba-Ahmed ya fice daga APC a kwanakin baya a inda ake zargin ya koma PDP kodayake dai bai bayyana a hukumance ba.
A yanzu haka kuma shine shugaban ma’aikatan Kakakin Majalisa Bukola Saraki babban mai adawa da Gwamnatin Buhari.
Daily Nigerian ta ruwaito DITV/Alheri Radio ta kori Umar Ridwan, mai gabatar da shirin ‘Matasa a Yau’ da kuma ‘Gari ya waye’ saboda ya yada labarin cewa ‘Shugaba Buhari ya biya tsaffin ma’aikata kudaden fansho’ lamarin da ya fusata mahukuntan kafar Yada Labaran suka dakatar dashi tsawon Sati Biyu.
A kwafin wasikar sallamar wacce majiyarmu ta mallaka hukumar DITV din ta bayyana sallamar Mista Umar ba tare da bayyana dalili ba. ‘Lamarin da masana ke ganin ya saba doka’
Amma kuma a cewar Umar Ridwan labarin da ya rubuta ne akan Buhari ya jawo aka dakatar dashi sannan da ya sake yin wani sai shugaban DITV ya fusata aka koreshi.
A nasu bangaren hukumar DITV-Alheri Radio ta bakin shugaban sashin labarai da al’amuran yau da kullum, Shuaibu Gimi yace ‘suna da ikon korar duk ma’aikacin da suka ga basu bukatarshi saboda zaman kansu suke yi’

No comments:

Post a Comment