El-Rufai Ya Ga Laifin Lai Mohammed, Ya Ce N3.5m Ba Na Ciyar Da El-Zakzaky Kawai Bane

El-Rufai ya ga laifin Lai Mohammed, ya ce N3.5m ba na ciyar da El-Zakzaky kawai bane
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai a ranar Alhamis, 15 ga watan Nuwamba ya bayar da wani Karin haske kan yadda gwamnatin tarayya ke kashe kimanin naira miliyan 3.5 a duk wata domin ciyar da shugaban kungiyar yan Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky wanda ke tsare.
El-Rufai ya ga laifin jawabin da ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed yayi lokacin da ya tarbi tawagar The Sun Publishing Limited, a jiya.
Idan zango Ku tuna Lai Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na kashe naira miliyan 3.5 duk wata wajen ciyar da El-Zakzaky.
Lamarin da ya haifar da cece-kuce inda mutane da dama suka soki gwamnatin tarayya kan kudaden da take kashewa a kansa.
A cewar gwamnan jihar Kaduna, naira miliyan 3.5 ba na ciyar da shugaban Shi’a bane kadai cewa hakan ya shafi duk wani tsaro ne da ake bashi a yayinda yake tsare.
Yace jami’an DSS da sojoji ne ke tsaron El-Zakzaky wanda hakan ya sanya suke zaune a inda yake ajiye sannan kuma gwamnati ce ke daukar dawainiyarsu.

No comments:

Post a Comment