Ganduje Na Neman Diyyar Bata Suna Naira Biliyan 3 Daga Jaafar Jaafar

Gwamann Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya shigar da karar kamfanin jaridar DAILY NIGERIAN tare da mawallafin jaridar Jaafar Jaafar, akan neman diyyar Naira biliyan 3 saboda  laifin fallasa bidiyon da ke nuna cewa, Gwamnan na karbar cin hanci daga hannun ‘yan kwangila.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta fitar da rahoton cewa, babbar kotun jihar ne ta sanar da hakan wata daya kenan bayan fallasa bidiyon.

No comments:

Post a Comment