Ganduje Na Shirya Yadda Za a Tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na shirya yadda za a tsige kakakin Majalisar dokokin jihar Kano Kabiru Alhassan Rurum da wasu shugabannin majalisar guda 6 sakamakon kafa kwamitin binciken badakalar da ake zargin Ganduje da tafkawa.
Wata majiya mai tushe ta shaidawa Daily Nigerian cewar Gwamnan yayi wata ganawar sirri da wasu makusantansa jim kadan bayan da ya koma Kano daga Abuja kan yadda za a tsige kakakin Majalisar dokokin.
Gwamna Ganduje na ganin cire Alhassan Rurum da sauran shugabannin majalisar shi ne dalilin da zai sanya a dena yi masa barazanar tsigewa.

No comments:

Post a Comment