Ganduje Zai Cigaba Zamansa A Gobe Da Kwamiti

Daga Imam A Saleh
Wasu kwararan majiyoyi sun tsegunta cewa kwamitin majalisar dokokin jihar Kano dake bincikar gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje akan zargin cin hanci zai cigaba da zaman sa a gobe duk da umarnin dakatar da binciken da kotu ta bayar.
Dama dai a gobe ne kwamitin ya tsara gayyato masu binciken sahihancin bidiyo domin tantance gaskiya ko kuma hada bidiyon kawai akayi.
Majiyar wacce ta nemi a sakaye sunan ta, tace yan majalisar sun harzuka matuka da jin matakin da kotun ta dauka, inda majiyar ta kara da cewa da yiwuwar majalisar ta kirawo taron gaggawa.
Majiyar ta rawaito cewa yan kwamitin na jaddada cewa doka ta basu damar aiwatar da wannan bincike tunda kudaden da ake zargin an bada cin hancin su na kwangila ne.
Bisa tsarin mulki dai doka ta baiwa majalisa damar aiwatar da bincike akan duk wasu kudade da aka karkatar matsawar majalisar ce ta amince tunda farko a aiwatar da aiyuka dasu.

No comments:

Post a Comment