Gwamnatin Najeriya Ta Mayar Da Martani Ga Atiku

Daga Datti Assalafy

Jiya Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa bayan ya dawo Nigeria daga kasar Dubai jami’an tsaron Nigeria sun masa bincike tare da mukarrabansa bayan saukarsa a tashar jirgin sama na Abuja wanda ya kwatanta hakan a matsayin cin zarafi.

Daga baya ministan sufurin jiragen sama Malam Hadi Sirika ya fito ya mayar da martani ga Atiku, yace ba gaskiya bane abinda Atiku ya wallafa cewa anci zarafinsa, yace abune na ka’ida duk wanda zai shigo Nigeria daga wata kasa ya sauka a filin jirgi sai an masa bincike, kuma jami’an kwastom da Immigrations da sauran jami’an tsaro na hadin gwiwa suke wannan binciken.

Hadi Sirika ya kara da cewa babu yadda za’ayi a wulakanta Atiku Abubakar a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban kasa har yanzu yana da ‘yancin a girmamashi.

Duk wanda ya taki gaskiya bai kamata yaji tsoro don an masa bincike ko za’a masa bincike ba.

Allah Ya kyauta.

The post Gwamnatin Najeriya Ta Mayar Da Martani Ga Atiku appeared first on ArewaBlog.Com™.

No comments:

Post a Comment