Hotunan Maulidin Sheik Ahmadu Tijjani A Gombe Da Dahiru Bauchi

MAULIDIN SHEHU AHMADU TIJJANI A JIHAR GOMBE
Daga Haji Shehu
A daren jiya Asabar, Mai Martaba Sarkin Gombe (Dr.) Abubakar Shehu Abubakar lll, ya karbi bakoncin Jikokin Shehu Ahmadu Tijjani wadanda suka zo gudanar da maulidin Shehu Ahmadu Tijjani a jihar Gombe karkashin jagorancin Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Sheriff Umar Morocco daya daga cikin Jikokin Shehu Ahmadu Tijjani, shi ya jagoranci Sallar Magrib da Isha kafun daga bisani su gabatar da zikiri a tsakanin Sallar Magrib da Isha..
Bayan kammala Sallar Isha, Shehinai da hadiman darikar Tijjaniyya sunyiwa Jikokin Shehu Ahmadu Tijjani tare da Sheikh Dahiru Usman Bauchi, rakiya zuwa cikin fadar mai martaba Sarki domin mika godiya da bangajiya tare da yi wa Sarki da jihar Gombe addu’a.

No comments:

Post a Comment