Kalli hotunan Asibitin Da Mai Martaba Sarkin Gombe Ya Ginawa Talakawansa

Katafaren Asibitin da mai martaba Sarkin Gombe Dr Abubakar Shehu Abubakar III, ya ginawa talakawan sa a unguwar Bolari dake cikin garin Gombe.
Kamar yadda kuke gani a cikin wadannan hotuna, ciki da wajen asibitin ne wanda yanzu haka aka kammala ginawa ana dakon isowar kayan aiki na zamani domin fara lura da lafiyar talakawan mai martaba Sarki.
Muna Addu’ar Allah ya biya mai martaba Sarki da mafificin alkairi, yasa sauran Sarakuna suyi koyi dashi wajen aikata alkairi wa talakawan su.
Daga Haji Shehu

No comments:

Post a Comment