Kotu Ta Ki Dakatar Da Yajin Aikin Kungiyar Kwadago

Kotun ma’aikatu ta kasa ta yi watsi da bukatar da aka shigar gabanta, na ta hana gamayyar kungiyoyin kwadago shiga yajin aikin da suke shirin tsunduma a gobe Talata, alkalin kotun mai shara’a Sanusi Kado, ya yi watsi da wata bukata ta daban, wacce aka bukaci ya umarci gwamnatin tarayya ta amince da Naira 30,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi.

Mai shara’a Kado ya ce ba wata ma’ana a sake yanke wani hukuncin hana kungiyar kwadagon shiga yajin aiki, saboda an riga da anyi hakan a ranar Juma’a, bayan da kotun ta yanke hukuncin bukatar da gwamnatin tarayya ta shigar gaban ta, gwamnatin tarayya ta dage akan Naira 24,000 a matsayin mafi karancin albashi, a yayin da gwamnoni kuma suka dage a Naira 22,500.
Tirka-tirka tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago ya sa gwamnatin ta shigar da bukata gaban kotun ma’aikatun ta kasa don hana ‘yan kwadagon shiga yajin aiki kamar yadda suka tsara, amma kungiyoyin kwadagon sunce kotun ba ta da hurumin hana su shiga yajin aikin da suka tsara

No comments:

Post a Comment