Kungiyar CAN Ta Bukaci Buhari Ya Saki Zakzaky Da Sambo Dasuki

Kungiyar CAN Ta Bukaci Buhari Ya Saki Zakzaky Da Sambo Dasuki

Daga Bilya Hamza Dass

Kungiyar Kiristoti ta Nijeriya (CAN) ta bukaci a saki jagoran harkar musulunci ta Nigeria (IMN), Shaik Ibrahim Zakzaky, da wasu wadanda kotu ta bada belinsu.

Shugaban na CAN, Rabran Samson Ayokunle, ya jagoranci wasu daga tawagar kungiyan ranar Juma’a 16/11/2018.

Ya nemi shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa, gwamnatin shi tana girmama doka da umurnin kotu ta hanyar bada belin kanar Sambo Dasuki (Rtd), da kuma Jagora ‘Yan Shi’ah, Malam Ibraheem Zakzaky, a sakesu kamar yanda kotu tayi umurni.

“Wannan zai rage tashin hankali a cikin Ć™asa kuma ya ba da daraja ga gwamnatinku tare da girmamawa daga al’ummomin duniya,” in ji Rev. Ayokunle.

Daga bisani ya yaba da yaki da cin hanci da rashawa na Gwamnatin Tarayya keyi

No comments:

Post a Comment