Kungiyar Shi’a Ta Karyata Gwamnati Kan Cewa Tana Kulawa Da El Zakzaky

__¥__
Kungiyar ‘Yan Shi’a sun karyata ikirarin Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed kan cewa gwamnati na kashe Naira milyan 3.5 a duk wata wajen ciyar da Shugaban Shi’a, Malam Ibrahim El Zakzaky inda kungiyar ta nuna cewa yanayin da malamin ke ciki babu alamun cikakken kulawa tare da shi.
Kakakin Kungiyar Ibrahim Musa ya ce, tun bayan da aka dawo da El Zakzaky Kaduna daga Abuja a watanni shidda da suka wuce, malamin ya koka kan rashin abinci Mai lafiya inda Kungiyar ta zargi wasu jami’an gwamnati da amfani da tsare malamin da ake yi wajen satar kudaden gwamnati.

No comments:

Post a Comment