Mummunar Maganar da Ronaldo Ya Fadi Akan Mancherster

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Roy Keane, ya bayyana cewa Ronaldo ya raina kungiyar Manchester United kuma bai kamata ace maganar daya fada ta fito daga bakinsa ba.
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Jubentus Cristiano Ronaldo ya ce tsohuwar kungiyarsa Manchester United ba ta cancanci yin nasara a wasan da ya gudana tsakaninsu a ranar  laraba ba, wasan da yaran Mourinho suka lallasa Jubentus da ci 2 da 1 har gida.
A cewar Ronaldo wanda ya zura kwallo a wasan cikin minti na 55 da fara wasa, Jubentus ce ta yi rawar gani a wasan kuma babu shakka da sun samu cikakken dama da sa a da sun ragargaji United.
Wasan dai shi ne karon farko da Jubentus ta sha kaye cikin wasanni 15 tun bayan sauya shekar Ronaldon zuwa gareta daga Real Madrid a watan Yulin da ya gabata kimanin watanni biyar kenan, haka zalika ita ke saman teburi a bangaren gasar Serie A, yayinda ta ke matsayin zakara a rukuninta na H a wasannin gasar cin kofin zakarun Turai.
A cewar Ronaldo dole ne ‘yan wasan na Jubentus su zage damtse la’akar da muhimmancin gasar matukar dai suna bukatar dage kofin na zakarun Turai a wannan shekara.
Ko a bara ma dai yayin gasar cin kofin zakarun Turai Jubentus din sai da ta kai wasan gab dana karshe amma Real Madrid mai rike da kambun ta yi waje da ita.
Roy Keane yace Ronaldo bai girmama tsohuwar kungiyar tasa ba kuma ba wanda zaiyi tunanin zai iya furta irin wanann maganar ga kungiyar da tayi masa komai.

No comments:

Post a Comment