Rigima ya Barke Tsakanin El-rufa`i Da PDP

Tun bayan da Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana sunan Balaraba a matsayin macen da zatayi takarar mataimakinsa a zaɓen 2019 jamiyyar PDP ta soma kumfar baki kan lamarin, inda tayi zargin Gwamnan da nuna wariyar addini kasancewar shi da mataimakiyar duk musulmai ne, sannan jamiyyar ta lashi takobin kayar dashi a zaɓe mai zuwa.
Sai dai, Gwamna El-Rufai ya mayar da martani.
Inda yace ai Peter Obi, wanda zaiyi takarar shugabancin ƙasa tare da Atiku, shine babban mai mai rura wutar wariyar addini musamman yadda yayi yunƙurin haramtawa musulmai hausawa zaman jiharsa lokacin da yake Gwamna.
Wannan martani sai ya sake tayar da hazo a fagen siyasar ƙasar nan, inda mambobin PDP irinsu Reno Omokri suka shiga bankaɗo tsoffin laifukan El-Rufa’in.
Zuwa yanzu dai, Reno Omokri, wanda yake tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasa Jonathan ne, yace El-Rufai ne babban mai nuna wariya, tunda har ya taɓa aike masa da saƙon imal da yake iƙirarin duk matayen kudancin ƙasar nan karuwai ne. Don haka idan har El Rufai ya musanta haka, to zai fitar da wancan saƙo ga manema labarai don kowa ya gani.
Saboda haka amsar Gwamna El-Rufai ce ta rage don ganin yadda lamarin zai kaya.

No comments:

Post a Comment