Ban Samu Albashi Ba Na Shekaru 8 — Gwamnan Osun Aregbesola

Gwamna mai barin gado na jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya ya ce tun da ya hau kan mulki tsawon shekara takwas bai taba karbar albashi ba.
Gwamna Rauf Aregbesola ya ce ba ya bukatar albashi lokacin da yake kan mulki saboda jihar ta ciyar da shi, ta ba shi abin hawa sannan ta ba shi wurin kwana tsawon lokacin da yake kan mulki.
“Tun da dai an biya min wadannan bukatu, ba na bukatar karbar kudi,” in ji shi.
Sai dai kalaman nasa sun sanya kokwanto a zukatan masu amfani da shafukan sada zumunta inda wasu suka ce karya yake yi.
Girman bushashar da jami’an gwamnatin Najeriya ke yi da kudaden gwamnati ya fito fili bayan da bayyana cewa alawus din sanatocin kasar kawai ya nunnunka albashin da babban ma’aikacin gwamnati ke dauka sau da dama.
Wani tsohon gwamna ya ce da a ce ‘yan Najeriya sun san albashin gwamna da ba za su iya barci ba don takaici.
Daya daga cikin masu amfani da shafukan sada zumunta wanda kalaman gwamnan suka ba shi haushi ya ce watakila Gwamna Aregbesola ya yi tsammani yana magana ne da “jarirai”, yayin da wani ya yi tambayar cewa: “Ta yaya wadannan kalamai za su kawo sauki ga wahalar da talaka ke ciki?”
A karshen wannan watan ne Rauf Aregbesola zai kammala wa’adinsa na biyu.
Mutumin da zai gaje shi, Alhaji Gboyega Oyetola, tsohon shugaban ma’aikatan gwamnatinsa ne, wanda ya lashe zabe da kyar a watan Satumba.

No comments:

Post a Comment