Shin Buhari Na da laifin Strike da Asuu T Tafi

Yajin Aikin ASUU: Laifin Buhari Ko Na Malaman Jami’o’i?
Daga Aliyu Usman Adam
__¥__
Kungiyar Malaman jami’o’i, ASUU ta shiga yajin aikin sai Baba-ta-gani a yau Litini.
Kungiyar malaman ta ce ta fara yajin aikin ne a dalilin kin rashin biya wa malaman jami’o’i bukatun su kamar yadda gwamnatin tarayya ta yi alkawari.
Malaman jami’o’in sun koka kan burus da gwamnati ta yi da su cewa gaba daya jami’o’in kasar nan ba za su ci gaba da aiki ba sai wada ta yiwu.
Wasu daga cikin bukatun kungiyar sun hada da rashin wadata jami’o’in da kudade domin gudanar da ayyukan su, sannan kuma da rashin maida hankali da gwamnati bata yi ba ga harkar ilimin jami’o’i a kasar nan.
A zahirin gaskiya gwamnati na neman gurguta harkar ilimi musamman a jami’o’i kasancewar tana nuna halin ko in kula a bangaren.
Ko me ya sa gwamnatin tarayya take wannan hali? Ko don ‘ya’yan jami’an gwamnati suna can kasashen waje suna karatunsu?
Ya kamata al’umma su sani cewa wannan yajin aikin da ASUU ke yi yana gurgunta ilimi ne kuma muddin aka cigaba da wannan abu mu ne ‘ya’yan talakawa zai shafa.
Ko don shi kansa mai gayya mai aikin, Shugaba Buhari ‘ya’yansa suna karatu a kasashen waje ne ya sanya aka ki biyawa ASUU bukatunsu?

No comments:

Post a Comment