Shugaban Kasa Bai Amince Da Biyan Naira 30,000 Ba

Fadar gwamnatin tarayya ta karyata rahotanni da suke yawo na cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da Naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi, bayan shugaban ya karbi sakamakon rahoton zaman tattaunawa da kwamitin’yan uku suka kammala a shekaranjia Litinin, daga wajen shugabar kwamitin, Ms Amal Pepple.
Wata majiya daga fadar shugaban kasan, ta tabbatar da cewa shugaban kasa bai amince da adadin ba a matsayin mafi karancin albashi, kamar yadda aka dinga yadawa a kafafun watsa labarai na kasar nan, illa iyaka dai shugaban kasa yana niyyar tabbatar da ya amince da sabon albashin da za a bayyana nan gaba, ko nawa ne kuwa.
Babu inda shugaban kasa ya nuna ya amince da Naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi a cikin jawabin shi, saboda ba aikin shi bane shi kada ya tabbatar da adadin a matsayin sabon albashi, dole sai majalisar ministoci da kuma ‘yan majalisun tarayya sun amince. Zuwa yanzu ba a kai ga bayyana wani tsayayyen adadi ba na mafi karancin albashin, amma dai ana sa ran majalisun tarayya zasu yi zama akai, don cimma matsaya akan matakin da shugaban kasa zai dauka.

No comments:

Post a Comment