Ummi Zeezee Ta Zama Shugabar Mata Ta Kungiyar Kamfe Din Atiku

Ummi Zeezee ta zama shugabar mata ta kungiyar kamfe din Atiku

Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta zama shugabar mata ta kungiyar kamfe din dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ta nuna a shafinta na sada zumunta na Instagram.

Shugaban gidauniyar tallafawa marasa galihu ta Atikun, Atiku Cares, Ambasada Aliyu Bn Abbas ne ya bayyana haka.

A sanarwar da ya fitar ta shafinshi na sada zumunta ya taya Ummi murna sannan yace suna fatan zata yi aiki tukuru zata kuma bi gida-gida dan tallata Atiku.

Instagram Photo

No comments:

Post a Comment