Wa Zai Maye Gurbin Ronaldo A Real Madrid?

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar Brazil, Cafu, ya bayyana cewa matashin dan wasa Binicius, dan kasar Brazil, zai iya maye gurbin Cristiano Ronaldo a Real Madrid idan har kungiyar ta tafiyar da dan wasan yadda yakamata.
Cristiano Ronaldo dai yabar Real Madrid ne inda yakoma kungiyar Jubentus kuma tun bayan komawarsa kungiyar ta Jubentus Real Madrid bata siyi dan wasan da zai maye gurbinsa ba dalilin dayasa Cafu yake ganin Binicius zai iya cike gurbin nasa idan har yasamu dama.
Real Madrid dai ta nemi manyan ‘yan wasa irinsu Edin Hazard da Neymar da Mbappe domin maye gurbin na Ronaldo amma duka basu samu ba hakan yasa kungiyar ta hakura da ‘yan wasan da take dasu a kungiyar.
“Tabbas Binicius matashin dan wasa ne kwarare wanda nan gaba zai zama baban dan wasa amma kuma bazance yakai Ronaldo ba sai dai mu tsaya muga abinda zai faru nan gaba idan ya sake girma” in ji Cafu Yaci gaba da cewa
“Ronaldo babban dan wasa ne wanda babu kamarsa kuma nan gaba za’a dade ba’a samu kamarsa ba amma shima Binicius dan wasa ne matashi wanda nan gaba zai zama babban dan wasa”
A karshe Cafu, wanda tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta AC Millan ne yace tsohon kociyan kungiyar da aka kora, Julian Lopetegui, yayi kuskure daya ajiye dan wasan a benchi a lokacin da kungiyar bata samun nasarori.
#Leadershipayau

No comments:

Post a Comment