Ya Karye A Kafarsa Ta Dama -Welbeck

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Unai Emery ya bayyana cewa dan wasan kungiyar, Danny Welbeck ya karye a kafarsa a wasan da kungiyar ta buga da Sporting Lisbon a ranar Alhamis din data gabata. Welbeck yaji ciwon ne a daidai minti na 25 da fara wasan lokacin da yayi yunkurin daukar wata kwallon da aka buga masa sai dai ya dawo ba a daidai ba kuma nan take yafadi kasa yana neman agajin likitoci.
Kafin dai a fitar da dan wasan daga filin wasa said a likitoci suka saka masa na’ura mai taimakawa nunfashi bayan da aka fahimci cewa ciwon da dan wasan ya samu babba ne kuma yana bukatar a tafi dashi asibiti nan take.
“Wannan ran ace ta bakin ciki ga kungiyarmu gaba daya da kuma magoya bayan Arsenal bisa wannan rashi da mukayi na babban dan wasa kamar Welbeck saboda ba wanda zaiyi zaton ciwon yakai girman haka” in ji kociyan kungiyar Yaci gaba da cewa “Da farko munyi zaton kawai bugewa yayi amma tunda muka fahimci cewa Welbeck ya kasa tashi muka tabbatar da cewa tabbas ba karamin ciwo bane kuma yana bukatar agajin likitoci”
Welbeck dai yasha fama da jinya kala-kala a kwanakin baya kuma daga baya yashawo kan matsalarsa kuma a jiya a ranar Alhamis kociyan tawagar ‘yan wasan kasar Ingila ya gayyaci ‘yan wasan da zasu wakilci kasar a wasannin da zasu buga a sati mai zuwa sai dai yanzu dole Welbeck bazai iya buga wasannin ba.

No comments:

Post a Comment