Wadansu Yan Majalisar Wakilai 2 Sun Fice Daga Jam’iyyar APC

‘Yan majalisar wakilai biyu sun bayyana ficewar su daga jam’iyyar APC mai mulki da safiyar yau Laraba, daga cikin ‘yan majalisar ya koma jam’iyyar PDP, amma daya dan majalisar har zuwa yanzu bai bayyana wacce jam’iyya zai koma ba.
]‘Yan majalisar sun mika wasikun ficewarsu daga jam’iyyar ne ga shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, in da ya Dogaran ya karanta anniyar ‘yan majalisar a zauren majalisar wakilai.
Babatunde Kolawale wanda yake wakiltar mazabar Akoko ta arewa masu yamma dake jihar Ondo, a wasikar shi ya bayyana aniyar shi ta komawa jam’iyyar adawa ta PDP.
Munkaila Kazzim, mai wakiltar mazabar tarayyya ta Abeokuta ta arewa dake jihar Ogun, a tashi wasikar bai kai ga bayyana wacce jam’iyya zai koma ba.
Dukkan mutanen biyu sun bayyana rikita-rikitar zabukkan fidda gwani na jam’iyyar APC, a matsayin dalilin su na ficewa daga jam’iyyar, inda Mista Kazzim ya zargi jam’iyyar da siyasar ubangida, ta inda in baka da ubangida ba zaka samu tikitin tsayawa takara ba.

No comments:

Post a Comment