`Yan Shi`a Sun Ja Kunnen Kakakin Rundanar `Yan Sandan Jihar Kano, SP Musa Majiya

‘Yan Shi’a Sun Nemi A Ja Kunnen Kakakin Rundanar ‘Yan Sandan Jihar Kano, SP Musa Majiya
Daga Bilya Hamza Dass
A wata takardar manema labarai da mabiya Shi’a suka fitar dauke da sanya hannun Ibrahim Musa Shugaban dandalin yada labarai na mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya a ranar 18/01/2018, sun bayyana cewa suna neman rundanar ‘yan sanda taja kunnen kakakinta akan kalaman kyama da ya keyi akansu.
Hakan yabiyo bayan sanarwan da kakakin yabar yan kan cewa an kama wani tsohon dan Shi’a yana hada baki da wani korarren dan sanda wajan karban kudin Jama’arsa bisa zalunci wanda yace suna cigaba da fadada bincike kan hakan, wanda tuni ‘yan Shi’an suka musanta zargin.
Takardar ta kara da cewa “Wannan ba shi ne karon farko da SP Majiya ke amfani da duk wata ‘yar damar da ya samu ba wajen bakanta Shi’a. Don haka muke kira ga rundunar ‘yan sanda ta tsawata masa, tare da tuna masa cewa ya guji amfani da matsayinsa wajen cimma wata manufa ta akidarsa.
Muna kuma kira ga jama’a da su yi watsi da maganganun da SP Majiya ya yi na nuna cewa Shi’a tana maraba da masu aikata miyagun laifuffuka. Sanannen abu ne cewa ‘yan Shi’a musulmin kwarai ne da suke gudun duk wani nau’in aikata muggan laifuka” Inji shi Ibrahim Musa.

No comments:

Post a Comment