Yariman Saudiyya Ne Ya Yi Sanadiyyar Kisan Dan Jarida Khashoggi

Sakamakon binciken da hukumar leken asirin CIA, ta kasar Amurka ta gudanar, ya nuna yarima mai jiran gado, Muhammad bin Salman na kasar Saudiyya ne ya bada umarnin kisan dan jarida mai adawa da manufofin kasar Saudiyya, musamman akan yakin da take yi da al’ummar kasar Yamen, wato Jamal khashoggi wanda ya bace a ofishin jakadancin kasar Saudiyya da ke birnin Sitanbul na kasar Turkiyya.
Sakamakon binciken na CIA, ya ci karo da na babban mai shigar da kara na kasar Saudiyya, wanda a nashi sakamakon ya daura laifin bacewar Khashoggi kan shugaban tawagar tattaunawa da kasar Saudiyya ta tura Turkiyya don ganin an taso kyayar Khashoggi zuwa Saudiyya don fuskantar hukunci kan kalubalantar manufofin gwamnatin kasar da yake yi.
Jaridar Washington Post ta buga sakamakon binciken da hukumar CIA din ta gudanar, inda shaidu masu karfi suka nuna, wata tawaga ta mutum 15 ta sauka kasar Saudiyya a jirgin gwamnatin kasar Saudiyyan, wannan tawagar ta mutum 15 ita ce ake ganin ta kashe Khashoggin a cikin ofishin jakadancin kasar Saudiyya da ke birnin Sitanbul.
Khashoggi wanda yake aiki da kamfanin jarida na Washington Post, ya je ofishin jakadancin kasar Saudiyya ne don amsar wasu takardu da zasu bashi damar auren wata da aka musu baiko da ita, wacce ‘yar asalin kasar Turkiyya ce, kasar Saudiyya ta musanta batun kisan Khashoggin a farko, amma daga baya ta amince cewa Khashoggin ya rasa ranshi sakamakon kokuwa da ya yi da mutum 15 a cikin ofishin jakadancin, amma daga baya kasar Saudiyyan ta sake canja magana.
A rahoton da hukumar CIA ta fitar, akwai hujjar muryar jakadan kasar Saudiyya a Amurka kuma kani ga Yariman kasar Saudiyyan, inda yariman yake umartar jakadan Saudiyya a Amurkan da ya tura Khashoggi ofishin jakadancin kasar Saudiyya dake Turkiyya, jakadan ya tabbatarwa Khashoggi ba wata matsala ya je ofishin jakadancin su na kasar Saudiyya don karbar takardun da yake bukata.

No comments:

Post a Comment